logo

HAUSA

WHO: Har yanzu alluran rigakafi suna ba da kariya daga sabbin nau’o’in COVID-19

2022-05-05 11:38:12 CMG Hausa

Kwararru a hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun jaddada cewa, har yanzu allurar rigakafin cutar COVID-19, na da matukar tasiri, har ma ga sabbin nau'o’in cutar da suka bulla a kasashen Afirka ta Kudu da Amurka.

Bayanan hukumar WHO sun nuna cewa, masu kamuwa da cutar COVID-19 a duniya na ci gaba da raguwa, inda aka samu rahoton mace-mace na mako-mako, mafi karanci tun watan Maris din shekarar 2020. Sai dai kuma babban darektan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadi a yayin wani taron manema labarai a jiya Laraba cewa, wadannan yanayin ba su ne ke bayyana cikakken halin da ake ciki ba.

Tedros Adhanom ya ce, sakamakon bullar sabbin nau’o’in cutar na Omicrons, ya sa muna samun rahoton masu kamuwa da cutar a Amurka da Afirka. Masana kimiyya na Afirka ta Kudu da suka gano nau’in Omicron a karshen shekarar da ta gabata, yanzu sun ba da rahoton bullar karin nau'ika biyu na Omicron, wato BA.4 da BA.5. a matsayin dalilin karuwar masu kamuwa da cutar a Afirka ta Kudu.

Ya kara da cewa, ya yi wuri a san ko wadannan sabbin nau’o’in cutar, na iya haifar da cututtuka mafi muni fiye da sauran nau'ikan Omicron, amma bayanan farko sun ba da shawarar cewa, rigakafin cutar, ita ce hanyar kariya mafi dacewa daga kamuwa da mummunan cuta da kuma kaiwa ga mutuwa. (Ibrahim Yaya)