logo

HAUSA

Yarjejeniyar Marrakesh ta fara aiki a kasar Sin

2022-05-05 13:23:29 CMG Hausa

Yarjejeniyar Marrakesh da aka kulla da nufin saukaka makafi, da nakasassu na gani da karanta kayayyakin takarda da aka wallafa a fili, wadda ta kasance yarjejeniyar hakkin dan adam daya kawai a duniya a fagen hakkin mallawafi ta soma aiki a yau Alhamis a nan kasar Sin. Hakan zai taimaka wajen kara kiyaye hakkin wadanda ke fuskantar matsalolin karanta abubuwa wajen samun daidaiton damar koyon al'adu da ilimi.

A watan Yunin shekatar 2013 ne, hukumar kula da ’yancin mallakar fasaha ta duniya, ta amince da wannan yarjejeniya, a wani taron diflomasiyya da aka gudanar a birnin Marrakech na kasar Morocco, kasar Sin ta kasance daya daga cikin rukunin kasashe na farko da suka sanya hannu. Yarjejeniyar ta fara aiki ne a ranar 30 ga watan Satumba na shekarar 2016, kuma a yanzu haka, kasashen da suka sanya hannu a kan yarjejeniyar sun kai 84.

Kasar Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyar ce bayan da aka zartas da ita, kuma a ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2016, ta kammala aikin gyaran dokar hakkin mallawafa, matakin da ya share fagen amincewa da yarjejeniyar. A watan Oktoban shekarar da ta gabata, aka kada kuri'ar amincewa da yarjejeniyar a yayin zama na 31 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, wato majalisar kafa dokokin kasar.

Sakamakon da aka gudanar kan nakasassu na kasar Sin karo na biyu, ya nuna cewa, akwai kimanin mutane miliyan 17.32 wadanda suke fama da matsalar gani a kasar, kuma wadanda ke fuskantar matsalar karanta abubuwa sun fi wannan adadin yawa. Bayan da yarjejeniyar Marrakesh ta fara aiki a kasar Sin, ana fatan za ta inganta tunani da al'adu na rukunin wadannan mutane, da karfafa matsayinsu na samun ilmi, da inganta yada kyawawan ayyuka na kasar zuwa ketare. (Mai fassara: Bilkisu)