logo

HAUSA

Babban aikin samar da ruwa na Sin zai amfani kaso 54% na al’ummun karkakar kasar

2022-05-05 20:04:57 CMG Hausa

Ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasar Sin ta sanar da cewa, a rubu’in farko na shekarar bana, gwamnati ta kammala babban aikin samar da ruwa ga yankunan karkara, wanda ya lashe kudin kasar har yuan biliyan 15.4, aikin da zai amfani karin mazauna karkara har mutum miliyan 4.29.

An yi hasashen cewa, ya zuwa karshen shekarar nan, adadin sassan karkarar kasar da ruwa zai isa gare su zai kai kaso 85%, yayin da alfanun babban aikin ruwa na yankunan karkarar kasar zai karu zuwa kaso 54 bisa dari. (Saminu)