logo

HAUSA

Zhao Lijian: Amurka ta kware wajen kitsa karairayi

2022-05-05 19:24:23 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya musanta zargin da Amurka ta yi, cewa wai Sin na taimakawa kasar Rasha a fannin yada bayanan bogi, yana mai cewa, irin wadannan kalamai na Amurka, manyan karairayi ne da kasar ke yadawa duniya, wanda hakan ya dada tabbatar da Amurka a matsayin wadda ta yi matukar kwarewa wajen kitsa kalaman bogi.

Zhao Lijian ya kuma ce Sin na kan bakan ta, na kin amincewa da matakin Amurka, na fakewa da batun kare hakkin bil adama, da amfani da karfin gwamnati wajen yiwa kamfanonin Sin matsin lamba.

Ya ce duk da yanayi na rashin daidaito da tabbashi, har kullum tattalin arzikin Sin na ci gaba da zaburar da tattalin arzikin duniya. (Saminu)