logo

HAUSA

Amurka na cin riba, yaya kuma kasashen Afirka?

2022-05-05 18:52:26 CMG Hausa

Shugaban bankin raya Afirka na AfDB Akinwunmi Adesina, wanda tsohon ministan noma ne a Najeriya, a yayin zantawarsa da shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari a kwanan baya, ya ce rikicin Rasha da Ukraine, ya haddasa hauhawar farashin alkama da kusan kaso 60 bisa dari a kasashen nahiyar Afirka. Adesina ya kara da cewa, tashin hankalin ya haifarwa duniya tarin kalubale, musamman ma kasashen Afirka, masu shigo da kaso mai yawa na abincin da suke bukata daga kasashen biyu.

Abin haka yake, daidai kamar yadda Adesina ya ce, barkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki, lamarin da ya haifar da munanan illoli ga tattalin arzikin duniya, musamman ma kasashen Afirka.

Amma kasancewarta kasar da ta hura wutar rikicin, kasar Amurka ta ci mummunar riba, inda kamfanoninta na samar da makamai suka ci riba bisa yawan makaman da aka saya daga wajensu.

Daga farkon shekarar 2022, sakamakon tasirin annobar Covid-19, an sha samun faduwar farashin hannayen jari a kasuwar hada-hadar kudi, amma wata guda bayan barkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraien, farashin hannayen jari na manyan kamfanonin samar da makamai na kasar Amurka, ciki har da Lockheed Martin da Raytheon, sun yi tashin gwauron zabi. (Mai Zane: Mustapha Bulama)