logo

HAUSA

Xi ya jagoranci taron jagororin CPC game da halin da ake ciki don gane da annobar COVID-19

2022-05-05 21:30:59 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron manyan jami’an kwamitin koli na hukumar siyasar JKS, game da halin da ake ciki don gane da annobar COVID-19.

Yayin taron na yau Alhamis, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kandagarkin annoba, da shawo kan yaduwar ta baki daya, muhimman matakai ne da ya wajaba a nacewa. Ya kuma yi kira da a tabbatar da aiwatar da manufar kawar da cutar COVID-19 baki daya. (Saminu)