logo

HAUSA

Charles Onunaiju: Kasar Sin Za Ta Raya Tattalin Arziki Ba Tare Da Tangarda Ba

2022-05-05 14:19:09 CMG HAUSA

Kwanan baya, yayin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua, Charles Onunaiju, darektan cibiyar nazarin kasar Sin dake Najeriya ya ce, sake barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a wasu sassan kasar Sin ta kawo wa kasar Sin barazana wajen raya tattalin arziki, amma Sin za ta raya tattalin arzikinta ba tare da tangarda ba, za ta kuma ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ba da jagora kan farfadowar tattalin arzikin duniya.

Charles Onunaiju ya kara da cewa, a shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta rika yiwa tsare-tsarenta kwaskwarima, da bullo da sabon salon raya kasa, inda ta mayar da kasuwannin gida a matsayin ginshiki tare da kara azama kan kasuwannin gida da waje, da sa kaimi kan sauyawa da kyautata kera kayayyakin masana’antu, yin sayayya da zuba jari, don haka kasar Sin tana da isasshen karfin tinkarar barazana da kalubale.

Charles Onunaiju yana ganin cewa, a kwanakin baya gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan tabbatar da kwanciyar hankali a harkokin kudi da gaggauta kafa kasuwar bai daya a duk fadin kasar, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin za ta tsara sabbin manufofi don daidaita barazana da kuma samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Charles Onunaiju ya nuna kyakkyawan fata kan kyautatuwar matsayin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. Yana mai cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta karfafa gwiwar zuba jari kan ababen more rayuwar jama’a a kasashen Afirka, lamarin da ya taimaka sosai wajen hada sassan Afirka waje daya. Sakamakon kaddamar da yankin ciniki maras shinge a nahiyar Afirka a hukumance, ya sa kasar Sin da kasashen Afirka za su samu damammaki masu dimbin yawa a fannonin ciniki, tattalin arzikin zamani da sabbin makamashi. (Tasallah Yuan)