logo

HAUSA

Tashar ruwa mai zurfi ta Lekki za ta samarwa Najeriya kudin shiga mai tarin yawa

2022-05-05 20:30:48 CMG Hausa

Ministan watsa labarai a tarayyar Najeriya Lai Mohammed, ya ce tashar ruwa mai zurfi da ake ginawa a birnin Ikkon jihar Lagos, za ta samarwa ‘yan kasar guraben ayyukan yi kimanin 170,000, tare da kudaden shiga ga gwamnati, daga nau’o’in haraji da yawan su zai kai dalar Amurka biliyan 201.

Lai Mohammed, ya bayyanawa manema labarai hakan a jiya Laraba, yayin da yake duba aikin ginin tashar ruwan ta Lekki, wadda kamfanin gine gine na kasar Sin na CHEC ke gudanarwa, a tsakiyar yankin cinikayya maras shinge na Lagos, mai nisan kilomita 60 daga gabashin birnin Ikko.

Bayan kammala aikin tashar ruwan mai zurfi, za ta kasance irin ta farko a Najeriya. (Saminu)