logo

HAUSA

MDD ta sanar da shirinta na samar da tsaftataccen makamashi mai araha nan da shekarar 2030

2022-05-05 10:43:28 CMG Hausa

Jiya ne MDD ta kaddamar da shirinta na samar da makamashi mai tsafta, da kuma araha ga kowa da kowa nan da shekarar 2030.

Stephane Dujarric, babban mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, shirin ya tanadi matakai na hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa guda 30, domin cimma gagarumin alkawarin da suka yi, a yayin babban taron tattaunawa kan makamashi da ya gudana a watan Satumban da ya gabata.

A cewar Dujarric, alkawarin ya kunshi baiwa karin mutane miliyan 500 damar samun wutar lantarki da kuma karin hanyoyin dafa abinci mai tsabta biliyan 1, da samar da guraben ayyukan yi miliyan 30 a fannin makamashin da ake iya sabuntawa da ingantaccen makamashi nan da shekara ta 2025. Ya kara da cewa, samar da makamashi mai araha nan da shekarar 2030 yana da mahimmanci wajen gaggauta magance matsalar yanayi da daina fitar da hayaki mai gurbata muhallinmu baki daya nan da shekarar 2050.

MDD dai ta sanar da yin hadin gwiwa don tallafawa wajen samar da makamashi da yadda kasashen Najeriya da Santiago na kasar Chile za su koma ga wannan tsari yadda ya kamata. (Ibrahim)