logo

HAUSA

Kasar Sin ta kafa tashar binciken yanayi mai sarrafa kanta mafi tsayi a duniya

2022-05-05 10:58:45 CMG Hausa

Jiya ne, masu binciken kimiyya na kasar Sin, suka kafa tashar sanya ido kan yanayin mai sarrafa kanta a tsawon mita 8,800 a kan tsaunin Qomolangma dake kan iyakar Sin da Nepal, abin da ya sanya ta zama mafi tsayi irinta a duniya.

A cewar cibiyar binciken tsaunin Tibet (ITP) dake karkashin cibiyar kimiyya ta kasar Sin (CAS), tashar ta maye gurbin tashar da aka kafa a tsayin mita 8,430 a gefen kudu da dutsen, wanda masana kimiya na kasashen Birtaniya da Amurka suka kafa a shekarar 2019, a matsayin mafi tsayi a duniya,

Baya ga sabuwar tashar nazarin yanayi, an kuma kafa kananan tashoshin sanya ido kan yanayi guda takwas a kan tsaunin na Qomolangma, daya daga cikin manyan ayyuka a jerin sabon aikin binciken kimiyya na kasar Sin, a kan kololuwar tsayin mita 8,848.86 da babu kamarsa a duniya.

Zhao Huabiao, wani mai bincike a cibiyar ITP, ya ce bayanan yanayin da aka sanya ido kansu, za su taimaka ga ayyukan binciken kimiyya da hawan duwatsu. (Ibrahim)