logo

HAUSA

Musulmai a jihar Xinjiang sun yi bikin karamar Sallah

2022-05-04 16:09:35 CMG Hausa

Musulmai a jihar Xinjiang ta kasar Sin, sun gudanar da shagulgula daban daban na bikin karamar Sallah a jiya Laraba.

Wasu musulmai a birnin Urumqi, sun gudanar da sallar idi ne a masallacin Yangxing mai tarihin sama da shekaru 120, karkashin matakan kariya da dakile yaduwar annobar COVID-19. A harabar masallacin Etigar dake Kashigar kuwa, mazauna na kabilu daban-daban ne suka yi kwalliya tare da gudanar da shagulgulan bikin ranar Sallar.

Ranar Sallah, rana ce da iyalai a jihar Xinjiang ke ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki, inda suke haduwa su yi ciye-ciyen nau’ikan abinci don murnar bikin. (Fa’iza Mustapha)