logo

HAUSA

MDD ta yi maraba da kwashe fararen hula daga masana’atar karafa ta Azovstal dake Mariupol

2022-05-04 15:59:40 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da kwashe fararen hula daga masana’antar karafa ta Azovstal dake Mariupol na kasar Ukraine.

Cikin wata sanarwa da aka fitar jiya, Antonio Guterres ya ce yana farin ciki da nasarar kwashe fararen hula sama da 100 daga masana’antar karafa ta Azovstal dake Mariupol, karkashin shirin MDD da kungiyar agaji ta duniya, Red Cross.

Ya kara da cewa, yana fatan za a ci gaba da hada hannu tsakanin Kiev da Moscow, domin ba fararen hula damar ficewa daga wuraren da ake yaki da kuma taimakawa wajen isa ga mutanen dake tsananin bukatar taimako.

Rahotannin kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, sojojin Rasha da Ukraine, sun bayyana a ranar Litinin cewa, sama da mutane 100 ne aka kwashe daga birnin Mariupol da aka yi wa kawanya. (Fa’iza Mustapha)