logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga babbar mai ba da gudunmuwar kudi ga MDD ta sauke nauyin dake wuyanta

2022-05-04 20:29:44 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga babbar mai bayar da gudunmuwar kudi ga MDD ta sauke nauyin dake wuyanta.

Dai Bing ya bayyana yayin kashi na biyu na zaman kwamiti na 5 na babban zauren MDD dake kula da harkokin gudanarwa da kasafin kudi cewa, babbar mai bayar da gudunmuwar kudi ga MDD ba ta sauke hakkin dake wuyanta ba cikin shekarun da suka gabata, yana cewa, ba ta yi wa sauran kasashe adalci ba. (Fa’iza Mustapha)