logo

HAUSA

Ofishin jakadancin dake Amurka ya karyata kalaman da Amurka ta yi kan rikicin Rasha da Ukraine

2022-05-04 15:44:25 CMG Hausa

Mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Amurka, ya mayar da martani kan tambayoyin da manema labaru suka yi jiya Talata, inda ya musanta bayanin da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi a ranar Litinin 2 ga wata cewa, wai jami'ai da kafofin watsa labaru na kasar Sin suna yada farfaganda da bayanan karya na Rasha, a yayin rikici tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.

Kakakin ya ce, matsayin kasar Sin kan batun Ukraine yana bisa gaskiya da adalci, kuma babu wani abin zargi a ciki. Idan ana batun yada bayanan karya ne, ya kamata Amurka ta yi tunani sosai a kai. Amurka ta kaddamar da yaki a kasashen Iraki, da Afganistan da Siriya tsawon shekaru, inda aka kashe fararen hula 335,000. Wannan ba labarin karya ba ne. Galibin kasashe a duniya suna bayar da shawarwari kan yadda za a warware rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ta hanyar tattaunawa da shawarwari, kuma ba sa son ganin lamarin ya kara ta'azzara, ko ma ya shiga wani hali, wannan ma ba labarin karya ba ne.

Jami’in ya ce, a watan Nuwamban shekarar 2021, kasar Amurka ta mika takardar bayanin aiki ga taron kasashen da suka kulla yarjejeniyar takaita yaduwar makaman kare dangi, tare da sanin cewa, kasar Amurka na da dakunan gwaje-gwajen kwayoyin halittu guda 26 da sauran cibiyoyin hadin gwiwa a Ukraine. Wannan ba bayanin karya ba ne. Don haka, ya kamata Amurka ta yi marhabin da al'ummomin duniya don gudanar da bincike cikin hadin gwiwa karkashin tsarin MDD da yarjejeniyar takaita yaduwar makamai masu guba. (Ibrahim)