logo

HAUSA

Masana kimiyyar Sin sun isa kolin tsaunin Qomolangma

2022-05-04 15:35:06 CMG Hausa

Tawagar masana kimiyya na kasar Sin ta “yanayin duniya na shekarar 2022”, ta yi nasarar hawa tsaunin Qomolangma mai tsawon mita 8,848 a yau Laraba, inda kashi na farko na tawagar ta isa kolin da misalin karfe 12:22 na rana, yayin da sauran suka cim musu bayan awa guda.

Mambobi 13 na tawagar da suka tashi da safiyar yau ne suka fara haye mita 8,000, inda 5 daga cikinsu suka kafa cibiyar tantance yanayi mai sarrafa kanta mafi tsawo a duniya da misalin karfe 11:11 na safiya, a kan yankin iyakar Sin da Nepal mai tsawon mita 8800. (Fa’iza Mustapha)