logo

HAUSA

Rahoto: Sinawa masu amfani da kayayyaki suna da kyakkyawan fata game da nan gaba

2022-05-04 15:14:16 CMG Hausa

Wani rahoto da kamfanin ba da shawara na kasa da kasa mai suna Ernst & Young (EY) ya wallafa ya bayyana cewa, Sinawa masu amfani da kayayyaki, sun fi nuna kwarin gwiwa game da makoma a nan gaba, sabanin raguwar amincewa da masu amfani da kayayyaki suka nuna a duniya.

A cewar rahoton, kimanin kashi 60 cikin 100 na Sinawa da aka tambaya sun yi imanin cewa, kudadensu za su karu a cikin shekara mai zuwa, fiye da matsakaicin kashi 48 cikin 100 na duniya, alkaluman dake da ke bin diddigin sauye-sauyen ra'ayi da dabi'un masu amfani da kayayyaki a kasuwannin duniya, tare da masu sayayya 18,000 a binciken da rahoton ya gudanar a duniya baki daya. .

Rahoton ya kara da cewa, a halin yanzu, kashi 43 cikin 100 na masu sayen kayayyaki a kasar Sin, sun ce halin da suke ciki na hada-hadar kudi ya samu kyautatuwa, sakamakon rage yawan amfani da kayayyaki da ake samu, wanda ya kai kashi 9 cikin dari fiye da matsakaici a duniya.

Rahoton ya ce, yayin da sauyin yanayi da ci gaba mai dorewa ke ci gaba da jan hankalin duniya, a hannu guda kuma, karin masu amfani da kayayyaki sun ce, suna sane da illar da dabi'ar amfani da su ke da kayayyaki ke haifarwa kan muhalli, kuma sun hada da shi a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi bukatunsu. (Ibrahim)