logo

HAUSA

An ceto mutum na tara a ginin da ya rufta a Changsha

2022-05-03 15:16:52 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, an yi nasarar ciro mutum na 9 da ya tsira daga baraguzan gini, sa'o'i 88 bayan da wani gini da wasu suka gina da kansu, ya rufta a lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin.

An dai garzaya da matar wadda aka ceto ta da misalin karfe 4:15 na safiyar yau Talata, zuwa asibiti.

Masu aikin ceto sun bayyana cewa, matar ta yi da buga abubuwa don aika sakonnin cewa, tana raye, kuma nan da nan suka gano ainihin inda ta ke, ta hanyar amfani da na’urorin gano wadanda ke raye da kuma bincike da hannu.

Ma’aikatan lafiya da ke aiki a wurin sun ce, matar tana cikin hayyacinta tana kuma ji da gani yadda ya kamata, saboda har yanzu tana iya magana da masu aikin ceton.

A ranar Jumma’a da misalin karfe 12 da mituna 24 da rana ne, ginin dake yankin Wangcheng a birnin Changsha na lardin Hunan ya rushe. An kuma yi imanin cewa, mutane 23 sun makale a cikin ginin, kamar yadda wani bincike na farko ya nuna. (Ibrahim)