logo

HAUSA

Xi ya karfafa gwiwar matasa da su taimaka wajen inganta dogaro da kai kan fasahar sararin samaniyar kasar Sin

2022-05-03 15:04:42 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karfafawa matasa da ke aikin sararin samaniya gwiwa, da su kara ba da gudummawa, wajen ganin kasar Sin ta kara dogaro da kai a fannin kimiyya da fasahar sararin samaniya.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin da yake amsa wasikar da tawagar matasan da ke aikin gina tashar binciken sararin samaniya a rukunin kimiyya da fasahar binciken sararin samaniya na kasar Sin suka rubuta masa. (Ibrahim)