logo

HAUSA

Tawagar bincike ta kasar Sin za ta yi kokarin kaiwa kololuwar tsaunin Qomolangma

2022-05-03 20:03:23 CMG Hausa

Tawagar bincike game da “yanayin duniya na shekarar 2022" ta kasar Sin, za ta yi kokarin isa kololuwar tsayin mita 8,848 na dutsen Qomolangma a gobe Laraba.

Tawagar tana dauke da tashoshin bincike yanayi masu sarrafa kansa da na'urorin radar, mambobi 14 na tawagar masu binciken na kasar Sin, sun tashi da karfe 2 na yammacin jiya Litinin. Rahotanni na cewa, wannan ita ce tafiya mafi mahimmanci da tawagar kwararrun masu hawan tsauni za su yi kan wannan manufa. (Ibrahim)