logo

HAUSA

Mutane 122 da kungiyoyi 33 sun karbi lambar yabo ta bikin ranar matasan kasar Sin

2022-05-03 20:17:31 CMG Hausa

A yau Talata, kasar Sin ta fidda jerin sunayen mutanen da suka samu lambobin yabo na ranar 4 ga watan Mayu, wato bikin ranar matasan kasar Sin, an ba da lambobin yabon mafi daraja ne ga matasan Sinawa gabanin gudanar da bikin ranar matasan sakamakon irin gudunmawar da suka baiwa kasa.

Jimillar daidaikun mutane 122 da kungiyoyi 33 ne suka samu nasarar shiga jerin sunayen. Kuma an zabo su ne daga bangororin kiwon lafiya, da injiniya, da sashen kashe gobara, da matukin jirgin sama, da masu binciken kimiyya, har zuwa malaman makarantu, da dalibai, da fagen wasanni, da jami’an kananan hukumomi, da manoma, da masu aikin jigilar kayayyaki. (Ahmad)