logo

HAUSA

EU ta zargi kamfanin Apple da kin shigar da abokan gogayyarsa tsarin biyan kudi na zamani

2022-05-03 16:13:27 CMG Hausa

An zargi kamfanin Apple da toshewa abokan takararsa hanyoyin tsarin biyan kudade na "tap-as-you-go" wanda ake amfani da tsarin wajen biyan kudade ta wayoyin hannu na iPhone, inda aka bayyana matakin da cewa tamkar neman yin matsin lamba ne ga abokan gogayyar kamfanin a fannin kimiyya.

Kungiyar tarayya Turai EU ta bayyana cewa, ta aike da sakon korafi ga kamfanin na Apple, tare da gabatar da cikakken bayani game da yadda kamfanin ya muzgunawa masu takara da shi a kasuwanni a tsarin biyan kudi ta wayoyin hannu da ake amfani da manhajar iOS.

Babbar jami’ar yaki da zamba ta kungiyar EU, Margrethe Vestager, ta ce, “Matsayar farko da aka cimma a yau tana da alaka da tsarin biyan kudade ta wayar hannu a shagunan sayayya, ta hanyar mayar da wasu tamkar saniyar ware.”

"Apple ya nuna rashin adalci wajen sanyawa abokan takara shamaki ga tsarin biyan kudade na Apple Pay wallets. Idan aka tabbatar da aikata wannan halayyar, to zai iya sauya matsayin da kamfanin ya jima a kansa, wanda yin hakan ya sabawa dokokinmu," in ji Vestager. (Ahmad)