logo

HAUSA

Sin ta fara aiki da dokar hana kamun kifi na bana

2022-05-02 15:53:43 CMG Hausa

Daga yau Lahadi, kasar Sin ta fara aiki da dokar hana kamun kifi na lokacin zafi na wannan shekarar a teku dake shiyyoyin arewaci, da gabashi, da kuma kudancin kasar, domin kiyayen tsaron tekuna da ake kama kifin.

Dokar haramcin kamun kifin, ta shafi tekun Bohai, da Rawayen teku, da tekun gabashin kasar, da tekun shiyyar kudancin kasar.

Ana sa ran dokar haramcin kamun kifin a tekun kudancin kasar Sin za ta zo karshe a ranar 16 ga watan Agusta. Kasar Sin ta fara kafa dokar haramcin kamun kifin a kowace shekara a tekun kudancin kasar Sin tun daga shekarar 1999, a matsayin wani mataki na kyautata tsaron tekunan kamun kifi da bunkasa ci gaban muhallin halittu.

Nan da kwanaki uku masu zuwa, jami’an tsaron tekun kasar Sin bangaren tekun kudancin kasar Sin, da sauran hukumomin yankin, za su fara aikin sintiri a manyan tekunan kamun kifi da tashoshin ruwa, domin tabbatar da kiyaye bin dokar yadda ya kamata.(Ahmad)