logo

HAUSA

Sin na da ikon samar da isasshen makamashi da take bukata

2022-05-02 16:06:29 CMG Hausa

Yayin da duniya ke fuskantar karin rashin tabbas, don gane da makomar kasuwar makamashi ta duniya, sakamakon tashe tashen hankula dake addabar wasu yankuna, kasar Sin ta sha alwashin samar da isasshen makamashi da al’ummar ta ke bukata.

Da yake tsokaci game da hakan, kakakin hukumar kididdiga ta kasar Fu Linghui, ya ce Sin na da ikon samar da makamashi mai inganci, wanda zai iya biyan bukatun kasar.

Jami’in ya ce, cikin rubu’in farko na shekarar nan ta 2022, Sin ta sarrafa kwal da adadin sa ya karu da kaso 10.3 bisa dari a shekara, zuwa tan biliyan 1.08, yayin da ta sarrafa danyen mai da adadin sa ya karu da kaso 4.4 bisa dari, sai kuma makamashin lantarki da kasar ta sarrafa, wanda adadin sa ya karu da kaso 3.1 bisa dari a shekara, inda ya kai kilowat tiriliyan 1.99.

Fu Linghui ya ce, kasancewar makamashi ginshikin raya tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma, zaman majalissar gudanarwar kasar Sin, ya yi kira da a kara inganta samar da shi, tare da kyautata amfani da nau’o’i daban daban na makamashin.  (Saminu)