logo

HAUSA

Masanin bankin Switzerland: Karfin tattalin arzikin Sin ya janyo hankalin masu zuba jari

2022-05-02 16:26:45 CMG Hausa

Fiorenzo Manganiello, wani masanin harkokin banki na kasar Switzerland ya bayyana a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kyakkyawar makomar da tattalin arzikin kasar Sin ke da ita, da yanayin karfin tattalin arzikin kasar, da kuma matakan bunkasa tattalin arziki na dogon lokaci da kasar Sin ta dauka, sun kasance a matsayin tushen dake kara janyo hankulan masu zuba jari na kasa da kasa.

A baya bayan nan, jaridar “British Financial Times: ta ba da rahoton cewa, bankunan zuba jari na kasa da kasa masu yawa, suna kara nuna sha’awarsu na shirin fadada huldar kasuwanci da birnin Shanghai, kuma matakan yaki da annobar COVID-19 da aka dauka a birnin ba su kashe gwiwar masu zuba jarin ba.

A cewar Manganiello, mamallakin kamfanin Lian Group, wani kwararren kamfanin zuba jari a Turai, ya ce wadannan shirye-shiryen fadada kasuwancin sun nuna cewa, kasar Sin ta kasance a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da tattalin arzikinta yake da karfin gaske a lokacin da ake fama da annoba, kuma makomar bunkasuwar tattalin arzikin tana da matukar karfi fiye da mafi yawan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Manganiello ya ce, yanayin tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da inganta, kuma bukatun da ake da su na kayayyaki kirar kasar Sin a cikin gida da ma kasa da kasa yana kara karuwa.

Kasar Sin za ta iya jure dukkan wahalhalu da haddura, kuma tana da kwarin gwiwar daidaita yanayin manyan bangarorin kasuwannin tattalin arziki, a cewar Manganiello. (Ahmad)