logo

HAUSA

An nuna damuwa kan matakin Amurka na dakile raguwar darajar kudi

2022-05-01 16:49:36 CMG Hausa

Rahoton jaridar “The New York Times” ya bayyana cewa, asusun kota kwana na tarayyar Amurka, ya dauki matakin kara ribar kudin ajiye a banki domin daidaita matsalar raguwar darajar kudi mafi tsanani da kasar ta gamu da ita a cikin shekaru sama da goma, lamarin zai sa Amurka ta kara fuskantar wahala yayin da take biyan bashin kasashe masu tasowa.

An lura cewa, alkaluman raguwar darajar kudin kasar ya karu daga kaso 7.57 bisa dari na watan Fabrairun bana zuwa kaso 8.54 bisa dari na watan Maris, wasu masanan tattalin arzikin kasar sun bayyana cewa, dalilin hakan shi ne domin shugaban kasar Joe Biden ya sa hannu kan shirin kashe kudin da yawansu ya kai dala sama da triliyan daya.

Sakamakon da aka samu daga binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata ya nuna cewa, al’ummun kasar sun fi mai da hankali kan matsalar raguwar darajar kudi, mutanen da aka yiwa binciken kaso 42 bisa dari suna ganin cewa, yanayin tattalin arzikin Amurka ba shi da inganci, kusan kaso 76 bisa dari sun lura cewa, yanayin yana kara tabarbarewa.

Rahoton “The New York Times” ya kara da cewa, abubuwan da suka faru a tarihin bil adama sun gaskanta cewa, matakin da asusun kota kwana na tarayyar Amurka ya dauka yana kawo mummunan tasiri ga kasashe masu tasowa a dogon lokaci.(Jamila)