logo

HAUSA

Katafaren kamfanin abinci na Sin zai wadata Beijing da abinci yayin da ake kokarin dakile cutar COVID-19

2022-05-01 16:44:04 CMG Hausa

Babban kamfanin samar da abinci na kasar Sin COFCO, ya fadada ayyukansa na samar da abinci a Beijing, kana ya kara yawan abincin da yake samarwa a sauran rassansa domin tabbatar da wadatar abinci, da daidaita farashin abincin, a babban birnin kasar Sin, a yayin da ake kokarin tinkarar yaduwar annobar COVID-19 a baya bayan nan.

Kamfanin ya riga ya aike da sama da tan 29,000 na muhimman kayan abinci ga kasuwannin birnin Beijing a watan Afrilu, da suka hada da shinkafa, garin filawa, taliya, man girki, nama da nau’ikan madara.(Ahmad)