logo

HAUSA

Kasar Sin na cike da imanin cimma burin ci gaban tattalin arziki na 2022

2022-05-01 16:29:34 CMG Hausa

Babban sakataren hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Zhao Chenxin, ya bayyana cewa, kasar tana da kwarin gwiwa kuma tana cike da imanin cimma burinta na samun ci gaban tattalin arziki a shekarar bana wato 2022.

Jami’in ya kara da cewa, za a daidaita tasirin da yaduwar cutar COVID-19 ke haifarwa ga kasar, kuma tattalin arzikin kasar zai ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri kamar yadda yake a baya.

Zhao Chenxin ya ce, ya dace a kara kyautata manufofin da abin ya shafa domin dakile sauye-sauyen da ake fuskanta, ta yadda za a tabbatar da ci gaban tattalin arziki a kasar ta Sin.(Jamila)