logo

HAUSA

An yi nasarar dakile hadarin bazuwar COVID-19 a unguwannin Shanghai

2022-05-01 15:59:10 CMG Hausa

 

Shugaban tawagar jami’an yaki da annobar COVID-19 na Shanghai, Gu Honghui, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, an samu nasarar daidaita matsalolin hadarin yaduwar annobar COVID-19 a unguwannin birnin Shanghai.

Gu, ya ce, adadin yaduwar cutar yana kara raguwa, yayin da alkaluman suka ragu daga makin Rt 2.27 zuwa 0.67.

Makin Rt ya kan nuna yanayin saurin yaduwar cutar COVID-19.

A cewar Gu, adadin yana cigaba da raguwa da kasa da maki guda cikin kwanaki 15 a jere.

An samu adadi mafi yawa na sabbin masu kamuwa da cutar a Shanghai a ranar 13 ga watan Afrilu, wanda ya kai 27,605, tun daga wancan lokacin kuma, adadin yayi ta raguwa.

A ranar Asabar, an samu rahoton sabbin masu kamuwa da cutar kimanin 788 a birni na Shanghai.

Kawo yanzu, wannan babban birni mai matsayin cibiyar kasuwanci ta kasar Sin ya samu jimillar masu kamuwa da cutar COVID-19 53,364, tun daga ranar 26 ga watan Fabrairu, kana an tabbatar cutar ta hallaka mutane 422 a birnin.(Ahmad)