logo

HAUSA

An binne tsohon shugaban Kenya Kibaki a mahaifarsa

2022-05-01 16:25:27 CMG Hausa

Emilio Mwai Kibaki, shugaban kasar Kenya na uku, wanda ya mutu a ranar 22 ga watan Afrilu yana da shekaru 90 a duniya, a ranar Asabar aka binne shi a garinsa na asali dake yankin Nyeri a tsakiyar Kenya.

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, wanda ya gaji shugaba Kibaki a shugabancin kasar a watan Afrilun shekarar 2013, yana daga cikin muhimman mutanen da suka halarci bikin binnewar, inda sojoji suka harba bindiga sau 19 domin girmamawa ga marigayin.

Da yake gabatar da jawabin nuna jinjina, Kenyatta ya yaba salon shugabancin Kibaki na kawo sauye-sauyen cigaba ga kasar, da aiki da basira, da nuna kishin kasa, da sadaukar da kai domin inganta rayuwar talakawan kasar, wanda ya dora kasar Kenya a kan turbar zama mai karfin tattalin arziki a shiyyar.

Keyatta yayi tsokaci cewa, “A yayin da muke shirin binne kwararren masanin tattalin arziki a makwancinsa, shugaba mai hangen nesa, ma’aikacin da ya sadaukar da kansa, ya kamata mu yi kokarin koyi da kyakkyawar halayyarsa, domin tabbatar da cikar burin wannan kasa, da kawo sauye-sauye da damammakin cigaba.”

Kenyatta, wanda wa’adin aikinsa na shugabancin kasa zai kare a watan Augusta kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada, ya kalubalanci shugabanni dasu rungumi tunani irin na Kibaki, kamar ingantaccen shugabanci, da kawo sauye-sauyen cigaban tattalin arzikin kasa, da kuma tabbatar da hadin kan kasa.(Ahmad)