logo

HAUSA

Xi ya jaddada bukatar raya jari yadda ya kamata a kasar Sin

2022-04-30 20:56:33 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a yi kokarin daidaitawa da habaka jari a kasar bisa kiyaye dokoki, tare da ba shi damar taka rawa a matsayin muhimmin bangaren samar da kayayyaki.

Xi ya yi kiran ne yayin da yake jawabi ga wani rukunin nazari na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar.  (Fa’iza Mustapha)