logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin: matakan Amurka na kawo tsaiko ga kokarin duniya na kyautata yanayin kare hakkin dan Adam

2022-04-30 18:06:43 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce a kokarinta na kare muradunta na danniya, Amurka ta matse kaimi wajen yayata siyasantar da batun kare hakkin dan Adan, lamarin da ya kawo tsaiko ga kokarin kyautata yanayin kare hakkin dan Adam a duniya.

Kakakin ma’aikatar, Zhao Lijian ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na jiya, inda yake mayar da martani ga “rahoton kare hakkin dan adam na kasa na 2021” da Amurka ta fitar a baya bayan nan, wanda ya janyo suka da adawa ga wasu kasashe da dama.

A cewar Zhao Lijian, rahoton na Amurka, ya yi wasu tsokaci marasa kan gado game da yanayin hakkin dan adam a kasashe da yankunan duniya 198, amma kuma ya ware Amurka. Ya kara da cewa, zarge-zarge marasa tushe game da hakkin dan Adam da Amurkar ke yi, ba zai kyautata yanayin da kasar ke ciki ta fuskar hakkin dan Adam ba, yana mai cewa, abun da zai yi shi ne, bankado munafurcinta da fuska biyu da take nunawa. (Fa’iza Mustapha)