logo

HAUSA

Kasar Sin ta lashi takobin kyautata ci gaban tattalin arziki yayin da take yaki da annoba

2022-04-30 18:12:45 CMG Hausa

Kasar Sin ta lashi takobin kyautata ci gaban tattalin arziki yayin da take ci gaba da aiwatar da matakan kandagarki da dakile cutar COVID-19. Haka kuma, za ta karfafa daidaita manufofin da suka shafi yanayin tattalin arziki domin cimma burakanta na raya tattalin arzikin da zamantakewa.

A jiya Juma’a ne ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ya gudanar da taro domin nazarin yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki yanzu haka da kuma sauran ayyuka masu ruwa da tsaki. Taron ya gudana ne karkashin jagorancin Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin kolin na jam’iyyar. (Fa’iza Mustapha)