logo

HAUSA

Bangarori daban-daban a Amurka sun yi kira a rage sanyawa kasar Sin harajin kwastam

2022-04-30 17:28:40 CMG Hausa

A kwanan nan, akwai bangarori daban-daban a kasar Amurka, da suka kara yin kira, da a rage buga harajin kwastam kan hajojin kasar Sin. Manazarta na ganin cewa, ci gaba da kara sanyawa kasar Sin haraji, zai haifar da tashin gwauron zabi na farashin kayayyakin yau da kullum, abun da zai kawo illa ga farfadowar tattalin arzikin Amurka.

Babban kwamitin kula da kasuwanci na Amurka da Sin ya fitar da sanarwa a kwanan baya, inda ya ce, kara sanya harajin kwastam kan hajojin da Amurka take shigarwa daga kasar Sin, zai sa masu sayayya da kamfanonin Amurka su biya harajin da ba na dole ba. A sabili da haka, idan aka soke karin harajin, zai rage farashin kayayyakin yau da kullum, al’amarin da zai saukaka rayuwar al’ummar Amurka.

Babban mataimakin shugaba mai kula da manufofin kasa da kasa na kungiyar ‘yan kasuwar Amurka, John Murphy ya wallafa wani bayanin dake cewa, karuwar tattalin arzikin Amurka na kara fuskantar matsi, ciki har da tsawwalar farashin kayayyaki, da matukar rashin ma’aikata da sauransu. Bayaninsa ya ce, rage harajin kwastam, ba daidaita mawuyacin halin da Amurkawa ke ciki kadai zai yi ba, wato hauhawar farashin kaya, har ma da inganta kwarewar masu kere-kere na kasar a fannin takara.

A nata bangaren kuma, sakatariyar baitulmalin Amurka, Janet L. Yellen ta bayyana cewa, a halin yanzu gwamnatin kasarta na nazarin manufofin kasuwancinta kan kasar Sin, kuma soke harajin da aka kara sanyawa hajojn Sin, abun lura ne.

Binciken jin ra’ayin al’umma ya nuna cewa, sakamakon hauhawar farashin makamashi da kayan abinci da na sauran kayan masarufi, al’ummar Amurka na kara nuna rashin jin dadi da gwamnatin Biden, al’amarin da ya sa ‘yan jam’iyyar Democrat ke fuskantar rashin kujeru masu rinjaye a yayin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, da za’a gudanar a watan Nuwambar bana. (Murtala Zhang)