logo

HAUSA

An yi gasar Sinanci tsakanin daliban jami’o’i a Najeriya

2022-04-30 17:13:32 CMG Hausa

A kwanan nan ne, cibiyar hadin-gwiwa da musayar harsunan Sin da na kasashen waje da ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, suka hada kai da kwalejojin Confucius dake jami’o’in Namdi Azikiwe da na Legas dake Najeriya, don gudanar da gasar Sinanci ta karshe ta kafar bidiyo ta daliban jami’o’in kasa da kasa karo na 21 mai suna “Chinese Bridge”.

Babban jami’in kula da harkokin al’adu dake ofishin jakadancin Sin a Najeriya, Li Xuda ya bayyana cewa, harshen Sinanci, hanya ce da ake bi wajen mu’amala da fahimtar juna tsakanin al’ummu. Li na fatan masu sha’awar koyon Sinanci a Najeriya za su kara azama wajen koyonsa, don bada tasu gudummawa wajen habaka sada zumunta tsakanin kasashen biyu.

Gasar ta bana ta kunshi tambayoyi da amsoshi kan ilimin kasar Sin, da gabatar da jawabi cikin harshen Sinanci da sauransu, inda mahalarta gasar suka samu yabo matuka, duba da yadda suka iya harshen, gami da sha’awar da suka nuna wajen koyonsa. (Murtala Zhang)