logo

HAUSA

Hajojin Afirka Na Matukar Jawo Hankalin Jama’ar Kasar Sin

2022-04-29 11:47:34 CMG Hausa

An bude bikin sayayyar hajojin Afirka ta yanar gizo karo na hudu a jiya, inda aka sayar da kayayyakin Afirka ga jama’ar kasar Sin ta yanar gizo. Manazarta suna ganin cewa, bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19, bikin ya sa kaimi ga yin sayayya a cikin kasar Sin, kana zai taimakawa raya hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka.

Tun daga shekarar 2019, an riga an yi irin wannan biki har sau uku, wanda ya jawo kamfanoni da masu kashe kudi da dama, wadanda suka halarci bikin, kuma hakan ya sa kaimi ga yin sayayya.

Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta yi, yawan kudin da aka samu a kasar Sin ta hanyar yin sayayya ta yanar gizo, a gun bikin na tsawon kwanaki 15 na shekarar 2021, ya kai kudin Sin Yuan biliyan 700.

An ce, a wannan karo za a gwada barasa, da kofi, da ruwan ’ya’yan itatuwa da sauransu daga kasashen Afirka ta Kudu, da Tanzania, da Ruwanda, da Benin da sauransu, a yayin bikin da aka shirya kai tsaye ta yanar gizo.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a cikin shekara daya da ta gabata, yawan cinikin da aka gudanar tsakanin Sin da Afirka ya karu bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19, kana yawansa ya karu da kashi 35.3 cikin dari, wanda ya kai matsayin koli a tarihi.

A cikin wannan adadi, yawan kayayyakin da aka shigar da su daga Afirka zuwa kasar Sin, ya karu da kashi 40 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. (Zainab)