logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da harin jami’ar Karachi a Pakistan

2022-04-29 10:45:22 CMG HAUSA

 

Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar a jami’ar Karachi ta kasar Pakistan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu Sinawa uku, da dan kasar Pakistan guda, tare da raunata wasu da dama.

A sanarwar da aka rabawa manema labarai, mambobin kwamitin sulhun sun yi Allah wadai da babbar murya ga harin ta’addanci, wanda kungiyar Majeed Brigade Baloch Liberation Army ta dauki nauyin kaddamarwa.

Mambobin kasashen kwamitin sulhun MDDr sun bayyana matukar juyayi tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma gwamnatocin kasashen Pakistan da Sin, kana sun yi fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka samu raunuka.

Kwamitin sulhun ya jaddada cewa, duk wani nau’in ayyukan ta’addanci mummunar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. (Ahmad)