logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kiran da a yaki ayyukan ta'addanci bayan kashe Sinawa uku a Pakistan

2022-04-29 20:38:15 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka shirya Jumma'ar nan cewa, kasar Sin ta bukaci dukkan kasashen duniya, da su hada kai wajen yaki da ayyukan ta'addanci da kuma kiyaye zaman lafiyar duniya.

Idan za a iya tunawa, malamai Sinawa 3 da wani dan kasar Pakistan daya ne suka gamu da ajalinsu, sakamakon fashewar wani abu a jami'ar Karachi ranar Talata, harin da dakarun 'yantar da Baloch ta dauki alhakin kaiwa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis, kwamitin sulhun MDD (UNSC) ya yi Allah wadai da babbar murya kan wannan mummunan harin ta'addanci na matsorata.

Zhao Lijian ya ce, sanarwar ta nuna yadda duniya ke nuna adawa da harin ta'addanci, tare da nuna juyayi ga Sinawa da harin ya rutsa da su.