logo

HAUSA

Mahukuntan Sin sun yi tsokaci kan yanayin tattalin arzikin kasar tare da yin sauye-sauye ga shirin raya kasa

2022-04-29 16:03:14 CMG HAUSA

 

A yau Juma’a babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, Xi Jinping ya jagoranci taron tattaunawa na hukumar siyasar kwamitin tsakiyar CPC domin nazartar yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da duba ayyukan dake shafar tattalin arzikin kasar.

Taron ya kuma yi garambawul kan hikimomin shirin raya ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 na shekarun 2021 zuwa 2025. (Ahmad)