logo

HAUSA

Zhang Jun: Sin aminiya ce ta gaskiya ga kanana da matsakaitan kasashe

2022-04-29 11:29:46 CMG HAUSA

 

A jiya Alhamis 28 ga watan nan ne MDD ta gudanar da taron tattaunawa na manyan jami’ai, don gane da batutuwan da suka shafi kananan kasashe, da cudanyar sassa daban daban, da kuma dokokin kasa da kasa.

Yayin taron, wakilin dindindin na kasar Sin a MDDr Zhang Jun, ya ce a halin da ake ciki yanzu haka, zaman lafiya da ci gaban duniya na fuskantar babban kalubale, da rashin tabbas, kana ginshikan dake haddasa yanayi na rashin tabbas na hadewa da juna, kuma dukkanin kasashe musamman kanana na shan matsin lamba sakamakon hakan.

Zhang Jun ya kuma jaddada cewa, domin shawo kan wadannan kalubale da ake fuskanta, ya zama wajibi a aiwatar da ainihin matakan cudanyar sassa daban bisa adalci. Ya ce tsarin duniya daya ne, kuma shi ne tsarin gudanarwar duniya da MDD ke jagoranta. Kaza lika ka’ida daya ce, kuma ita ce wadda kasa da kasa suka aminta da ita karkashin ka’idar gudanarwa ta kasa da kasa.

Wakilin na Sin ya kara da cewa, rigingimu da ake fuskanta a shiyyoyin duniya, na nuni ga ainihin manufar cudanyar sassa daban daban, wanda bai dace ya zamo wata dama ta kafa rukunonin siyasa, ko kananan kawance domin ingiza fito na fito, ko bude sabon fagen cacar baka ba. Maimakon hakan ya kamata cudanyar sassan duniya ta ba da zarafin kare tsarin gudanarwar duniya da MDD ke jagoranta, da ka’idar kasa da kasa da sassan duniya suke amincewa.

Daga nan sai Zhang Jun ya jaddada salon diflomasiyyar kasar Sin, wanda ya ce har kullum na dora muhimmanci ne ga samar da daidaito. Ya ce “Mu abokai ne na gaskiya ga tarin kanana da matsakaitan kasashe, kuma har kullum muna tare da su. Kananan kasashe su ne mafiya yawa a duniya cikin jimillar kasashe mambobin MDD 193. Ya kamata a ce wadannan kananan kasashe ne za su fayyace ko tsarin cudanyar da ake gudanarwa a yanzu ya dace ko akasin haka. Kananan kasashe na taka muhimmiyar rawa a fannin magance mummunan tasirin sauyin yanayi, da aiwatar da matakan wanzar da ci gaba, da tabbatar da doka da oda a matsakin kasa da kasa”.  (Saminu)