logo

HAUSA

Sin: Aiwatar da yarjejeniyar takaita yaduwar makamai masu guba yadda ya kamata na fuskantar kalubale da dama

2022-04-29 20:56:02 CMG Hausa

A ranar 29 ga Afrilu ne, ake cika shekaru 25 da fara aiwatar da yarjejeniyar takaita yaduwar makamai masu guba. Yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi nuni da cewa, shekaru 25 da suka gabata, yarjejieniyar ta taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Ya kuma yi nuni da cewa, har yanzu yarjejeniyar tana fuskantar kalubale da dama:

Zhao ya bayyana cewa,har yanzu ba a lalata tarin makamai masu guba da Amurka ta mallaka ba, kuma Amurka ce kasa daya tilo da har yanzu ke rike da tarin makamai masu guba, lalata makamai masu gubar da Japan ta yi watsi da su a kasar Sin, sun jima da wuce gona da iri, wanda ke matukar barazana ga rayuka da dukiyoyin al'ummar kasar da kiyaye muhallin halittu. Wasu kasashe na amfani da makamai masu guba a kasar Syria, da sauran munanan batutuwa wajen yin magudi na siyasa, wanda haka katsalanda ne ga ayyukan hukumar hana amfani da makamai masu guba ta duniya. Ya kamata kasashen da abin ya shafa su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, tare da kiyaye ikon yarjejeniyar hana yaduwar makamai masu guda cikin hadin gwiwa.