logo

HAUSA

Adadin masu harbuwa da COVID-19 a Shanghai na kara raguwa cikin kwanaki 6 a jere

2022-04-29 11:08:20 CMG HAUSA

 

Mahukunta a birnin Shanghai na kasar Sin sun ce, adadin masu harbuwa da annobar COVID-19 a birnin na kara raguwa tsawon kwanaki 6 a jere, kuma ana duba yiwuwar sassauta matakan kulle da birnin ke ciki, da tallafawa fannin masana’antu wajen komawa bakin aiki.

A ranar Laraba, birnin mai yawan al’umma da ya kai miliyan 25, ya tabbatar da harbuwar mutanen da suka nuna alamar cutar su 1,292, da wadanda ba su nuna alama ba su 9,330, wanda hakan ya nuna raguwar sabbin masu harbuwa da ita cikin kwanaki 6 a jere.

Mahukunta a birnin sun ce mazauna yankunan da ba su da masu dauke da cutar ko kadan, na iya yin zirga-zirga zuwa wurare kebabbu.

Tun bayan fara aiwatar da tsauraran matakan rufe sassan birnin a ranar 28 ga watan Maris, birnin dake gabashin kasar Sin, ya samu jimillar adadin wadanda suka harbu da COVID-19 sama da 500,000.  (Saminu Hassan)