logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe mayakan masu tsattsauran ra’ayi 23 a yakin da suke da ta’addanci

2022-04-29 11:01:57 CMG HAUSA

 

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa, sama da mayakan kungiyar masu tsattsauran ra’ayi 23, ciki har da manyan kwamandojojin kungiyar ISWAP aka kashe, a ayyukan sintiri na yaki da ta’addanci da rundunar sojojin ta kaddamar a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar cikin makonni ukun da suka gabata.

Bernard Onyeuko, kakakin hukumar sojojin Najeriyar ya bayyanawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, ayyukan sintirin da sojojin suka kaddamar sun yi nasarar tilasta mayakan ’yan ta’adda  1,159 sun mika wuya, kana sun kubutar da mutane 619 da mayakan suka yi garkuwa da su.

Onyeuko ya ce, sojojin sun gudanar da ayyukan sintirin ne a jahohin Borno da Taraba, inda suka samu gagarumar nasara.

A cewarsa, cikin mayakan ’yan ta’addan da suka mika wuya tare da iyalansu, sun hada da kananan yara 627, da mata 367, da maza 164 inda aka mika su ga hukumomin da suka dace. (Ahmad)