logo

HAUSA

Yawan GDP na kasar Amurka na rubu’in farko na bana ya ragu da kashi 1.4 cikin dari

2022-04-29 11:48:51 CMG Hausa

Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin cinikayya ta kasar Amurka ta fitar a jiya, an ce, yawan GDP na kasar Amurka a rubu’in farko na shekarar 2022, ya ragu da kashi 1.4 cikin dari, bisa yawansu a duk shekara da aka yi hasashe. Wannan ne yawan adadin mafi karanci da kasar ta samu a cikin shekaru 2 da suka wuce, bayan barkewar cutar COVID-19.

A halin yanzu, dalilin da ya sa tattalin arzikin Amurka ya ragu shi ne gaza samar da kayayyaki yadda ya kamata, da karuwar hauhawar farashin kaya, da kuma rashin isasshen kwadago a kasar. (Zainab)