logo

HAUSA

Jakadan Sin a Najeriya ya halarci bikin kaddamar da aikin horaswa

2022-04-28 13:57:11 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya halarci bikin kaddamar da aikin horar da kwararrun ma’aikata a fannin aikin sadarwa, a ranar 25 ga watan da muke ciki. Aiki ne da kamfanin Huawei na kasar Sin, da ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani ta Najeriya suka yi hadin gwiwar gudanarwa. Sauran manyan kusoshin da suka halarci bikin kaddamarwar sun hada da ministan sadarwa da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani na Najeriya Isa Pantami, da wakilan wasu jami’o’i guda 8, da dai sauransu.

Cikin wani jawabin da ya gabatar wajen bikin, jakada Cui na kasar Sin ya ce, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya jaddada bukatar karfafa hadin kan kasar Sin da kasashen Afirka, wajen aiwatar da wasu manyan ayyuka guda 9 na raya kasashen nahiyar Afirka, yayin taron ministoci karo na 8, karkarshin laimar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bara.

Domin aiwatar da manufofin da shugaban ya gabatar ne, aka fara gudanar da aikin horaswa na wannan karo, wanda zai ba da gudunmawa ga yunkurin zurfafa hadin kan kasashen 2.

A nashi bangare, minista Pantami ya ce, kasancewarta kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, Najeriya na da makoma mai haske, inda bangaren tattalin arzikin kasar mai alaka da fasahohin zamani ke samun ci gaba cikin matukar sauri. Ya ce Najeriya ta gode wa kasar Sin bisa taimakon da ta samar mata, musamman a fannin raya fasahohin zamani.

Wannan aiki na horaswa, zai ba daliban jami’o’in Najeriya su dubu 30, damar shiga kwas na musamman da kamfanin Huawei ya tsara, cikin shekaru 3 masu zuwa. Kana za a kara yawan jami’o’in da ake hulda da su zuwa 300, domin gudanar da wannan aiki. (Bello Wang)