logo

HAUSA

Ya kamata kasashen Sin da Afirka su hada kai wajen zakulo tsarin demokuradiyyar da ta dace da yanayin kasashensu

2022-04-28 21:01:04 CMG Hausa

An gudanar da taron karawa juna sani ta yanar gizo tsakanin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisun dokokin kasashen Afirka masu magana da harshen Faransanci daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Afrilu da muke ciki. Sama da 'yan majalisar dokoki 90 daga kasashen Afirka 22 masu magana da harshen Faransanci ne suka halarci taron. Mahalarta taron sun yi tattaunawa mai zurfi kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, tare da yin na’am da fa’idar tsarin demokuradiyyar jama'ar kasar Sin, sun kuma yi imanin cewa, ya kamata Sin da Afirka, su hada kai wajen nazarin tsarin demokradiyya da ya dace da yanayin kasashensu, da ba da gudummawa wajen ci gaba da kyautata jin dadin rayuwar jama'a, da inganta tsarin dangantakar demokiradiyar kasa da kasa.