logo

HAUSA

Ana kara samar da guraben aikin yi yadda ya kamata a rubu’in farko na bana

2022-04-28 11:03:42 CMG HAUSA

 

Bisa kididdigar da hukumar kwadago ta al’ummar Sin ta samar, mazaunen birane da garuruwa na samun guraben aikin yi yadda ya kamata a rubu’in farkon bana, karkashin nagartattun manufofi na samar da guraben aikin yi, ciki hadda kara karfin ba da horaswa, da nuna goyon baya ga sana’ar kirkire-kikire, da kara ba da hidimma a wannan fanni da sauransu, inda yawan karin mutanen da suka samun guraben aikin yi ya kai fiye da miliyan 2.85, wanda ya kai kashi 26% na adadin burin da aka tsara.

Hukumar ta nuna cewa, za a ci gaba da ingiza manufofi don tabbatar da samar da guraben aikin yi, ciki hadda rage buga haraji da kudin inshorar al’umma, da goyon bayan bunkasuwar kanana da matsakaicin kamfanoni, da ba da kulawa ga sana’o’i da suka fi fama da illar cutar COVID-19, da tsai da manufofin taimakawa matasa masu kammala karatu daga makarantu wajen samun guraben aikin yi, da daidaita matsalolin da dalibai, masu kammala karatu da manoma, da mutanen da suke fita daga kangin talauci, da wadanda suke rasa aikin yi da dai sauransu, da mutanen da suke da wuyar samun guraben aikin yi. 

Ban da wannan kuma, hukumar za ta kara karfin ba da horo, da hidimmomi don tabbatar da manufofin tabbatar da samun guraben aikin yi. (Amina Xu)