logo

HAUSA

An kaddamar da aikin binciken dutsen Qomolangma yau

2022-04-28 10:33:19 CMG Hausa

A yau Alhamis, wata tawagar nazarin tsaunuka masu fadi na Qinghai da Tibet na kasar Sin, ta sanar da kaddamar da aikin binciken dutsen Qomolangma, ko kuma “Everest” a Turancin Inglishi.

Yao Tandong, shugaban tawagar binciken, ya ce za a yi amfani da wasu fasahohin zamani wajen gudanar da bincike, kan yadda dumamar yanayin duniya ke yin tasiri kan muhallin dutsen Qomolangma, da canzawar yawan iska mai dumama yanayi da ake samu, da yadda dan Adam ke jure muhalli mai wahala, da dai sauran bangarori da dama, ta yadda za a gabatar da nagartacciyar dabara, ta kare muhallin dutsen Qomolangma.

Wannan tawaga ta kunshi kungiyoyi 16, da masana kimiyya da fasaha, da kwararru masu fasahar hawan duwatsu fiye da 270.

Kasar Sin ta gudanar da ayyukan binciken dutsen Qomolangma mafi tsayi a duniya fiye da sau 6, tun daga shekarun 1950. Kana bincike na wannan karo, zai zama karon farko da dan Adam ke gudanar da nazari na kimiya a yankunan dake kusa da kolin dutsen, wanda tsayinsu ya wuce mita 8000. (Bello Wang)