logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Manufofin kasa da kasa ba ka’idojin wani rukuni ne ba

2022-04-28 20:25:15 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya amsa tambayar da aka yi masa a yau Alhamis, game da kalaman sakatariyar harkokin wajen Birtaniya, Liz Truss, inda a cewarsa, ya dace ka’idojin kasa da kasa su zama manufofin alakokin kasa da kasa daidai bisa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, maimakon su zama ka’idoji na wasu gungun mutane ko wasu rukunoni na musamman.

A ranar Laraba ne, sakatariyar harkokin wajen Birtaniya, Liz Truss ta zargi kasar Sin cewa, wai ba ta la’anci kutsen da Rasha ta yiwa Ukraine ba, kana da wuya kasar Sin ta ci gaba da zama babbar kasa, in ta ki amincewa da gudanar da harkokinta bisa ka’idoji.

Game da wannan furucin nata, Wang Wenbin ya jaddada cewa, matsayin gwamnatin kasar Sin kan batun Ukraine, har kullum a bayyane yake, kuma Sin na da nata ra’ayi na zabin bisa gaskiyar lamarin da ya faru. (Murtala Zhang)