logo

HAUSA

Sin: Ba wanda zai iya tsoma baki cikin shawarar kulla yarjejeniyar hadin kai a fannin tsaro tsakanin Sin da tsibiran Solomon

2022-04-28 15:17:46 CMG HAUSA

 

Yau alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya halarci taron kaddamar da cibiyar hadin kai game da tinkarar sauyin yanayi tsakanin Sin da tsibiran tekun Pacific ta kafar bidiyo, tare da ba da jawabi. 

Game da jita-jita, da kuma bakin fentin da a kwanan baya aka rika shafawa shawarar kulla yarjejeniyar hadin kai a fannin tsaro tsakanin Sin da tsibiran Solomon, Xie Feng ya bayyana matsayin da Sin take dauka a gun taron, ga shugabannin kasashen yankin, da jakadun dake kasar Sin.

Xie Feng ya nuna cewa, kasashen biyu na da ikon tattaunawa kan yarjejeniyoyin hadin kai tsakaninsu, wanda ya kasance ikon mulkin kasa ne, kuma ya dace da dokar kasa da kasa. Ya ce kasashen biyu sun gudanar da hadin kai a fili cikin adalci, matakin da bai sabawa sauran hadin kai da Solomon ke yi da kasashe daban-daban ba, ya kuma dace da moriyar Solomon da ma duk yankunan kudancin tekun Pacific.

Ban da wannan kuma, Xie ya kara da cewa, tekun Pacific dandali ne na hadin kan kasa da kasa, a maimakon wurin takara a fannin siyasa. Ya ce Sin ta bunkasa huldarta da kasashen a wannan yanki, bisa ka’idar cimma moriyar juna, da samun bunkasuwa, tare da shimfida zaman lafiya, kuma ko kadan ba za ta nemi nuna karfin tuwo ko yin babakere ba. (Amina Xu)