logo

HAUSA

Yawan jarin ketare da aka zuba wa kasar Sin ya karu sosai

2022-04-28 10:38:20 CMG Hausa

Hukumar kula da kudin musanya ta kasar Sin, ta gabatar da wasu alkaluma a jiya Laraba, wadanda suka nuna cewa, an samu wani yanayi na daidaituwa tsakanin kudin musanya da kasar Sin ta samu, da wanda ta biya, cikin rubu’i na farko na bana.

An ce cikin wannan wa’adi, yawan kudin musanya da aka zuba wa kasuwannin kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 107, adadin da ya zama mafi yawa a tarihi.

Wasu masana ilimin tattalin arziki sun nuna cewa, yayin da kasar Sin ke ci gaba da aiwatar da matakai don tabbatar da karuwar tattalin arziki cikin gida, za a fara ganin alamar gudanar tattalin arzikin kasar cikin wani nagartaccen yanayi, kana kudin musanya da kasar za ta samu, da wanda ta biya, za su ci gaba da zama cikin daidaito. (Bello Wang)